Shugaban Jami’ar Bayero da ke Kano, Farfesa Haruna Musa, ya ƙaddamar da Kwamitin bada Shawara na Masana’antu (SIAB) na Cibiyar nazarin harkokin Noma a Yankunan Tsandauri (CDA), inda ya naɗa shugabar i WOFAN Dakta Salamatu Garba, a matsayin shugabar kwamitin.
Da yake jawabi a wajen taron, shugaban jami’ar ya ce ƙwararrun da aka naɗa a cikin kwamitin za su ƙara ƙarfafa ƙarfin cibiyar wajen bunƙasa tsaron abinci da ƙirƙire-ƙirƙiren noma a Najeriya.
Ya bayyana aikin a matsayin mai muhimmanci kuma mai ɗauke da nauyi, tare da yi wa mambobin addu’ar samun shiriya a yayin gudanar da wannan aiki.
Haka kuma ya taya WOFAN, Cibiyar CDA da al’ummar jami’ar murna kan ƙaddamar da shirin SIBLING cikin nasara.
Ya nuna godiya bisa rabon tallafin shinkafa ga ma’aikatan ƙananan matakai 2,617 na jami’ar, yana mai cewa wannan tallafi ya zo a kan lokaci kuma ya yi tasiri matuƙa.
A cewarsa, jami’ar na matuƙar godiya da goyon bayan da aka bai wa ma’aikatanta.
Tun da farko, Daraktan Cibiyar Nazarin harkokin Noman Yankunan Tsandauri Farfesa Sanusi Gaya Mohammed, ya gabatar da mambobin kwamitin da aka sake fasaltawa.
Ya bayyana cewa kwamitin ya ƙunshi mambobi 12 — bakwai daga waje da biyar daga cikin jami’a — waɗanda aka zaɓa domin ba da shawarwari na masana’antu da kuma jagoranci kan shirye-shiryen cibiyar da dorewar ayyukanta na dogon lokaci.
A nata jawabin a madadin kwamitin, Dakta Salamatu Garba ta ce sun ji daɗin amincewar da aka ba su na gudanar da wannan muhimmin aiki.
Ta yi alƙawarin cewa kwamitin zai tallafa wa manufofin cibiyar tare da tabbatar da ta samu ƙarin tasiri.
Ta bayyana aikin a matsayin gata da ƙalubale, tana mai cewa yin aiki a cibiyar da ke da ƙwararru masu yawa na buƙatar haɗin kai da taimakon juna.
Ta ƙara da cewa kasancewarta mace kaɗai a cikin kwamitin na ƙara mata nauyi, amma ta nemi haɗin kai da shawarwarin takwarorinta domin ciyar da jami’ar gaba fiye da yadda ake zato.
Sauran mambobin kwamitin daga waje sun haɗa da Alhaji Nasiru Wada, Manajan Darakta na kamfanin Esoterra Investment Ltd kuma Magajin Garin Kano; Alhaji Ali Safiyanu Madugu, Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na kamfanin Dala Foods Nigeria Limited; Mohammed Salasi Kibiya, Wakilin Ƙasa na IFDC; Alhaji Yusuf Ado Kibiya, Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Chimande Nigeria Limited; Dakta Donald Madukwe na OCP; da Abubakar Garba Ibrahim na kamfanin SILVEX International Limited.
Mambobin cikin gida kuwa sun haɗa da Farfesa Sanusi Gaya Mohammed, Daraktan CDA; Farfesa Jibrin Mohammed Jibrin, tsohon Daraktan CDA; Farfesa Murtala Mohammad Badamasi, Mataimakin Darakta (Horo); Dakta Mustapha Mohammed Bello, Mataimakin Darakta (Bincike); da Dakta Amina Lawan Mustapha, Mataimakiyar Darakta (Wayar da Kai da Wallafe-wallafe).
Bayan ƙaddamarwar, kwamitin ya gudanar da zamansa na farko a cibiyar, inda suka tattauna muhimman batutuwa ciki har da dabarun dorewar ayyukan cibiyar bayan ƙarewar tallafin Bankin Duniya.
Dakta Salamatu Garba ce ta jagoranci zaman a matsayin shugabar kwamitin.













































