Mutane biyu sun mutu, biyar sun jikkata yayin rikici a zaɓen gunduma na APC a Ondo — ’Yan sanda

Burnt car 750x430

Rundunar ’yan sandan Jihar Ondo ta ce mutane biyu sun rasu yayin da wasu uku suka jikkata a lokacin zaɓen gunduma na jam’iyyar APC a jihar.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Abayomi Jimoh, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Akure, inda ya ce lamarin ya faru ne a Idanre da ke Ƙaramar Hukumar Idanre.

Ya ce ba a kama kowa ba har yanzu, amma an tura jami’an tsaro na musamman domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi tare da hana sake ɓarkewar rikici.

A cewarsa, rundunar ta samu kiran gaggawa daga jami’in ’yan sanda na yankin Idanre kan wasu hare-hare da wasu mutane suka kai a ranar 18 ga Fabrairu da misalin ƙarfe 11:05 na safe.

Ya ce rahoton ya sa jami’an rundunar suka ɗauki matakin gaggawa.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Adebowale Lawal, ya tura jami’an tsaro na musamman domin ƙarfafa tsaro a yankin.

Daga bisani, Lawal tare da Kwamandan Hukumar NSCDC na jihar, Oluyemi Ibiloye, suka jagoranci haɗaɗɗiyar tawagar jami’an tsaro zuwa wurin da lamarin ya faru.

Matakin da suka ɗauka ya taimaka wajen dawo da zaman lafiya da doka a yankin.

A yayin rikicin, rahotanni sun nuna cewa an kai hari kan wasu mutane biyar da ba a tantance ba, sannan an ƙone wata mota.

Mutane uku sun samu raunuka daban-daban kuma ana kula da su a asibiti, yayin da aka tabbatar da mutuwar wasu biyu bayan an kai su asibiti.

Mai magana da yawun rundunar ya ce kwamishinan ’yan sandan ya ziyarci waɗanda suka jikkata domin duba halin da suke ciki tare da ba su tabbacin goyon bayan rundunar.

Ya ƙara da cewa ana ci gaba da bincike domin gano musabbabin harin tare da kamo waɗanda suka aikata wannan mummunan laifi.

Rundunar ta buƙaci al’ummar jihar Ondo su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da harkokinsu cikin lumana, tana mai tabbatar da cewa an ɗauki matakan tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a faɗin jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here