Mai safarar muggan kwayoyi ya kasayar da hodar iblis a filin jirgin sama

imgonline com ua twotoone k60WneR4DLdt
imgonline com ua twotoone k60WneR4DLdt

Jami’an hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa sun kama wani dan Najeriya da ya dawo daga kasar Brazil, Okolie Paulinus Nwabueze a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja bisa laifin shigo da hodar iblis casa’in da biyu wanda ya ci kuma daga karshe ya kasayar da ita, kwanaki kadan bayan da hukumar ke tsare da shi.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa an kama Mai dillacin miyagun kwayoyin ne dan shekaru 53 da haihuwa da ya fito daga kauyen Mmaku na karamar hukumar Awgu ta jihar Enugu a ranar Juma’a 2 ga watan Satumba bayan isowarsa daga jirgin Qatar da ke kan hanyar zuwa Brazil-Doha-Abuja.

Ya yi ikirarin cewa ya bar Najeriya zuwa kasar Mozambik a shekarar 2004, daga karshe ya koma Brazil a 2017, inda ya samu takardar izinin zama kafin ya yanke shawarar shigo da haramtacciyar hodar iblis kan kudi dala 4,000.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar Femi Babafemi ya fitar akarshen mako.

Daga wasu sassan kasar nan, an kama wata mata mai dauke da juna biyu, Haruna Favour, mai shekaru 25 a Karamar hukumar Auchi ta jihar Edo a ranar Juma’a 9 ga watan Satumba dauke da fetamine guda 82.

A Gombe, an kwato wasu kullin hodoji dubu 119 na kwayar tramadol, D5 da Exol5 daga hannun wasu dillalan magunguna guda biyu, Nasiru Abubakar mai shekaru 22, da Umaru Bayero me lakabin Hadiza a lokacin da jami’an hukumar suka kai samame kan shagunansu a babbar kasuwar Gombe ranar Talata 6 ga watan Satumba.

A jihar Kogi, an kama wani da ake zargi mai suna Paul Ali mai shekaru 47 a hanyar Okene zuwa Abuja dauke da kwalabe 1,404 na maganin Codeine mai nauyin kilo 190.94 da kuma ampoules na allurar pentazocine 2,040 daga Onitsha zuwa Sokoto.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here