Manyan Ƴan Majalisar Birtaniya sun yi mubaya’a ga sabon sarki

FB IMG 16628159282528241
FB IMG 16628159282528241

Manyan Ƴan Majalisar Birtaniya ciki har da Firaiminista Liz Truss sun yi mubaya’a ga Sabon Sarki Charles III a wani zama na musamman da majalisar ƙasar ta yi.

Kakakin Majalisar Wakilan Birtaniya Lindsay Hoyle shi ne ya buɗe zaman bayan yin mubaya’a, bayan nan sai kuma Sir Peter Bottomley, wanda shi ne ɗan majalisa da ya fi daɗewa a majalisar.

Hoyle ya bayyana cewa sakamakon ƙarancin lokaci, ƴan majalisa ƙalilan ne kawai za su iya yin mubaya’ar.

Truss na daga cikin waɗanda suka yi mubaya’ar inda suka rantse cewa za su yi biyayya ga sabon sarki Charles III da magadansa kamar yadda doka ta tanada.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here