Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya roƙi ’yan Najeriya da su yafe masa idan ya yi musu wani laifi, yana mai kira ga al’umma su rungumi haɗin kai, zaman lafiya da gyaran ɗabi’a yayin da ake fara watan Ramadan.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin buɗe Tafsirin bana a masallacin Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Shugaban ya yi nuni da dacewar Ramadan da azumin Kiristoci na Lent, yana mai cewa hakan na tunatar da al’umma muhimmancin ƙa’idodi iri ɗaya da addinai ke koyarwa.
“Ramadan ya zo daidai da Lent, yana tunatar da mu ƙudurorinmu na bai ɗaya kan sadaukarwa, ladabi, addu’a da kame kai,” in ji shi.
Ya ce azumi bai kamata ya tsaya ga ƙin ci da sha kawai ba, yana mai cewa dole ne ya ƙunshi tausayi, yafiya, ayyukan alheri da kuma ƙaunar bil’adama.
Tinubu ya buƙaci ’yan Najeriya na dukkan addinai su yi addu’a domin zaman lafiya tare da goyon bayan ƙoƙarin da ake yi na yaƙi da ta’addanci, fashi da makami da sauran matsalolin tsaro.
Babban Limamin Masallacin Fadar Shugaban Ƙasa, Abdulwahid Suleiman, ya gode wa Allah da Ya ba Musulmi damar sake shaida Ramadan.
Ya kuma yaba da jagorancin Tinubu tare da yi masa addu’ar samun hikima, lafiya da ƙarfi, haka kuma ya roƙi Allah Ya ba Najeriya zaman lafiya, kwanciyar hankali da wadata.












































