ICPC ta tsare El-Rufai sakamakon ci gaba da binciken da ta ke yi masa

El Rufai of Kaduna State (1)

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa mai zaman kanta, ICPC, ta ce ta tsare tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

A wata sanarwa da shugaban sashen yaɗa labarai na hukumar, J. Okor Odey, ya fitar, ya ce an tsare shi ne a daren Laraba dangane da wasu bincike da ake yi.

Sai dai bai bayyana takamaiman dalilin binciken ba.

Sanarwar ta ce El-Rufai yana hannun hukumar zuwa ƙarshen aikinta na ranar Laraba, 18 ga Fabrairu, 2026, kuma ana tsare da shi ne bisa bincike da ake yi.

A ranar Litinin ne ya gabatar da kansa a hedikwatar EFCC bayan gayyata kan zargin almundahanar kuɗaɗe a lokacin mulkinsa daga 2015 zuwa 2023.

A 2024, Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta tuhume shi da karkatar da Naira Biliyan 423 na kuɗaɗen jama’a da kuma wankiyar kuɗi, tare da neman hukumomin yaƙi da rashawa su bincike shi.

A makon da ya gabata, jami’an tsaro sun yi yunƙurin kama shi a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja bayan dawowarsa daga Alkahira, Masar.

El-Rufai ya zargi cewa an ba jami’an DSS umarnin kama shi.

DSS ta shigar da ƙara mai tuhuma uku a kansa kan zargin katsalandan a tattaunawar waya ta mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro.

Rahotanni sun bayyana cewa an tsare shi ne bayan ya kwashe kwanaki biyu a hannun EFCC.

Har yanzu ba a tabbatar ko DSS ce ta miƙa shi ga ICPC domin ci gaba da bincike ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here