Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya gana da shugabannin Kungiyar Kwadago ta ƙasa NLC a fadar gwamnati da ke Abuja da daren Talata, a ƙoƙarin dakatar da shirin zanga-zangar ƙasa baki ɗaya da ƙungiyar ta shirya sakamakon matsalar rashin tsaro.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa NLC ta ayyana shirin gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar, tana mai danganta matakin da tabarbarewar halin tsaro a Najeriya.
Shugaban NLC Joe Ajaero ne ya jagoranci tawagar shugabannin ƙwadago zuwa ganawar da aka yi ta sirri, inda bayan kammala taron ya bayyana cewa har yanzu ba a yanke hukunci na ƙarshe kan ci gaba da zanga-zangar ba.
Ya jaddada cewa duk wani matsayi da NLC za ta ɗauka ana yanke shi ne bisa shawarar haɗin gwiwa, ba bisa ra’ayin mutum ɗaya ba, tare da bayyana cewa za su koma su tattauna abubuwan da shugaban ƙasa ya gabatar kafin ɗaukar mataki na gaba.
Labari mai alaƙa: Kungiyar Kwadago NLC ta bayyana dalilan zanga-zangar 17 ga Disamba kan matsalar tsaro
A cewarsa, shugabannin NLC za su sake zama da sassafe domin nazari da tantance sakamakon ganawar da suka yi da shugaban ƙasa, sannan su fitar da matsaya a kai.
Ganawar ta samu halartar shugaban ƙungiyar gwamnonin APC Hope Uzodimma na jihar Imo, gwamnan jihar Edo Monday Okpebholo, gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris, da kuma ƙaramar ministar ƙwadago Nkeiruka Onyejeocha.
Ana sa ran NLC za ta sanar da matsayarta kan zanga-zangar bayan kammala shawarwarin cikin gida.












































