Kungiyar Kwadago ta kasa NLC ta bayyana cewa zanga-zangar ƙasa baki ɗaya da ta shirya gudanarwa a ranar 17 ga Disamba na da nufin jawo hankalin jama’a da masu ruwa da tsaki kan tabarbarewar matsalar tsaro a Nijeriya tare da tilasta ɗaukar matakan gaggawa domin magance ta.
Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya bayyana hakan a jihar Gombe a ranar Asabar yayin da yake ganawa da ‘yan jarida bayan ganawarsa da gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, kan batutuwan da suka shafi ƙwadago da walwalar ma’aikata.
Ya ce zanga-zangar za ta matsa lamba ga gwamnati ta ɗauki matakan da suka dace kan matsalar tsaro, yana mai jaddada cewa halin da ake ciki yanzu ya shafi kowane ɗan Nijeriya ba tare da la’akari da matsayi ko sana’a ba.
Ajaero ya bayyana cewa ayyukan ‘yan bindiga da laifukan tashin hankali ba su dace da al’adar Nijeriya ba, kuma wajibi ne kowa ya yi Allah wadai da su domin dakatar da abin da ya bayyana a matsayin mummunar hanyar da ƙasar ke bi.
Karin labari: Alƙalai ba sa cikin umarnin janye musu ƴan sanda – Babbar alkaliya ta ƙasa
Ya ƙara da cewa matsalar tsaro na lalata tattalin arziki tare da rage damar Nijeriya ta jawo masu zuba jari na cikin gida da na waje.
Ya kuma bayyana cewa rashin tsaro na shafar ma’aikata matuƙa, inda ake sace su a kai a kai wasu kuma ake kashe su, yana mai kawo misali da wani lamari a jihar Kebbi inda aka kashe wani malami tare da sace ‘ya’yan ma’aikata.
Ya ce irin waɗannan abubuwa na nuna tsananin barazanar da rashin tsaro ke haifarwa ga rayuwar al’umma.
Shugaban NLC ya buƙaci gwamnati ta gano masu aikata laifukan tare da kawo ƙarshen matsalar baki ɗaya, yana mai jaddada cewa zanga-zangar na nufin nuna goyon bayan jama’a ga gwamnati wajen yaƙi da rashin tsaro.
Ya kuma yi kira ga haɗin kan kowa, inda ya ce, satar mutane don neman kuɗin fansa na lalata ƙimomin ƙasa da haɗin kan al’umma, tare da buƙatar faɗaɗa shirye-shiryen tallafin jin ƙai domin mafi ƙarancin albashi kaɗai ba zai wadatar wajen rage wahalhalun rayuwa ba.
NAN













































