Alƙalai ba sa cikin umarnin janye musu ƴan sanda – Babbar alkaliya ta ƙasa

CJN Justice Kudirat Kekere Ekun

Babbar alkaliya ta ƙasar, Mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta bayyana cewa alƙalai ba sa cikin umarnin shugaban ƙasa na janye ‘yan sanda da ke tare da manyan mutane masu muhimmanci, inda ta jaddada cewa an ware jami’an shari’a kai tsaye daga wannan mataki.

Ta bayyana cewa umarnin na daga cikin matakan da aka ɗauka domin tinkarar tabarbarewar tsaro a ƙasar, amma ta nuna a fili cewa an keɓe alƙalai daga aiwatar da shi, domin tabbatar da tsaro da ‘yancin aikin shari’a.

Wannan bayani ya fito ne a cikin sanarwa da mai taimaka mata kan harkokin yaɗa labarai, Tobi Soniyi, ya fitar bayan Babban alkalin jihar Taraba, Mai shari’a Joel Agya, ya nuna damuwa cewa an janye ‘yan sandan da ke kare alƙalan jihar.

Karanta: Da ɗumi-ɗumi :Jirgin sama ya yi hatsari a filin jirgin saman Kano

Mai shari’a Agya ya yi gargadi cewa wannan janyewar na haifar da barazanar tsaro ga alƙalai, musamman masu sauraron shari’o’in manyan laifuka, siyasa, ta’addanci da cin hanci da rashawa, tare da cewa hakan na iya barazana ga ‘yancin shari’a da tafiyar da zaman kotu cikin tsari.

A martaninta, Soniyi ya bayyana cewa babbar alkaliya ta ƙasa ba ta da masaniya kan janye ‘yan sandan da ke kare alƙalai, yana mai cewa irin wannan mataki bai dace da umarnin ba tun da an ware alƙalai a sarari, kuma babu wani babban alkalin jiha da ya kai rahoton makamancin haka.

A halin da ake ciki, kwamishiniyar ‘yan sanda ta jihar Taraba, Betty Isokpan, ta musanta janye ‘yan sandan da aka ɗora wa alƙalai, inda ta bayyana cewa tsarin ya shafi rakiyar ‘yan sanda ga manyan mutane ne kawai, ba jami’an da ke aikin kotu ko waɗanda ke kula da gidajen alƙalai ba, domin kowane kotu na da jami’in ‘yan sanda na aiki a lokacin zaman shari’a.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here