Kudirori arba’in da biyu na gyaran kundin tsarin mulkin kasar nan a ranar Laraba ya tsallake karatu na biyu a majalisar wakilai.
Daga cikin kudurorin har da na cire rigar kariya da aka baiwa mataimakin shugaban kasa, gwamnoni da mataimakansu domin dakile cin hanci da rashawa, kawar da rashin adalci, da kuma kara kaimi a ma’aikatun gwamnati.
Wannan ya biyo bayan kudurorin gyara kundin tsarin mulkin kasar nan guda 39 da suka kai matakin karatu na biyu a zauren majalisar a ranar Talata.
Wasu muhimman shawarwarin da suka karfafa yiwa dokokin karatu na biyu a ranar Laraba sun haɗa da:
Kudirin dokar da za ta sauya kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na 1999, don tabbatar da kariyar da aka baiwa shugaban kasa, cire rigar kariya da aka baiwa mataimakin shugaban kasa, gwamnoni, da mataimakansu, don dakile cin hanci da rashawa, kawar da rashin adalci, da kuma kara daukar matakai a ma’aikatun gwamnati.
Kudirin dokar da za ta sauya kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 don raba ofisoshin babban lauyan gwamnatin tarayya, babban lauyan wata jiha, da ofisoshin ministan shari’a na gwamnatin tarayya da kuma kwamishinan shari’a na gwamnatin jiha.
Kudirin dokar da za ta sauya tanade-tanaden kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999, na bai wa matan Najeriya ‘yancin cin gashin kai, ya fayyace mafi karancin matasa da mata da za a nada a wasu mukamai.
Sauran kudirorin sun hada da na kirkiro jihar Ijebu, jihar Ife-Ijesa, jihar Tiga, jihar Orlu, da kuma jihar Etiti.
Sai dai ba a yi muhawara kan kudurorin ba, kuma wannan ya kawo jimlar dokokin zuwa yanzu sun tsallake karatu na biyu zuwa 81.













































