Rundunar ‘yan sandan jihar Rivers ta tabbatar da kashe wasu da ba a tantance adadinsu ba da suka yi yunkurin lalata bututun mai a yankin Aluu da Rumuekpe a jihar Rivers.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ribas, CP Olugbenga Adepoju, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Fatakwal a ranar Talata, inda ya bayyana cewa wadanda ake zargin sun mutu nan take.
Ya bayyana cewa, wannan farmakin na daga cikin ayyukan hadin gwiwa da sauran jami’an tsaro domin kare jihar.
Adepoju ya ci gaba da cewa, bayan nasarar da aka samu, jami’an tsaro sun zarce zuwa karamar hukumar Onelga a ranar 19 ga watan Maris, inda suka dakile wani harin bam na wasu yan ta’adda.
Karin karatu: Gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago sun yi barazanar ɗaukar mataki kan dokar ta-ɓaci a Rivers
A yayin samamen, ya ce an kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu wajen haifar da fashe fashe, da sauran abubuwan fashewa.
Adepoju ya kuma bayyana cewa akwai bukatar kara yawan jami’an tsaro domin dakile ayyukan ta’addanci a fadin jihar.
A cewarsa, jami’an tsaro na hadin gwiwa sun kafa dakin kula da ayyuka na Jiha domin sa ido da kuma dakile barazanar tsaro cikin gaggawa.
Jami’in ‘yan sandan ya kuma bayar da gargadi kan ci gaba da fasa bututun mai da iskar gas da sauran ababen more rayuwa a jihar, inda a cewar sa jami’an tsaro za su gano tare da kamawa da kuma gurfanar da mutanen da ke aikata irin wadannan abubuwan da suka sabawa doka. (NAN)