Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da murabus din kwamishinansa na sabuwar ma’aikatar tsaron cikin gida da ayyuka na musamman Manjo Janar Muhammad Inuwa Idris mai riyaya.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Talatar da ta gabata, gwamnan ya bayyana matukar jin dadinsa ga Janar din sojan mai ritaya bisa ayyukan da ya yi wa jihar a cikin kankanin wa’adin da ya yi, inda ya bayyana irin gudunmawar da ya bayar wajen fara aiki a ma’aikatar.
Gwamna Yusuf ya kuma mika sakon fatan alheri ga tsohon kwamishinan, inda ya bayyana shi a matsayin ma’aikacin gwamnati mai kishin kasa kuma dan Najeriya mai kishin kasa.
“Muna godiya ga Manjo Janar Muhammad Inuwa Idris mai ritaya bisa jajircewa da bayar da gudummawar da yake bayarwa ga ci gaban jihar Kano tun daga lokacin da ya fara aikin soja, muna masa fatan samun kwanciyar hankali da kuma gama aikin gwamnati lafiya.” Inji Gwamnan.