Gamayyar kungiyoyin farar hula a Kano, sun yi Allah wadai da cin zarafin wasu ‘yan jarida biyu da ake zarginsu da yin wani labarin na bayyana ra’ayi wanda aka buga, inda suka bayyana matakin a matsayin wani yunkuri na tsoratar da ‘yan jarida da kuma dakile ‘yancin fadin albarkacin baki.
A wata wasika da suka aike wa kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, gamayyar kungiyoyin fararen hula a jihar Kano, sun bayyana cewa kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya shigar da kara inda ya bukaci a kama Buhari Abba Rano mawallafin internet da kuma Isma’il Auwal, dan jarida mai zaman kansa kuma memba a kungiyar farar hula ta Kano.
A cewar wasikar, korafin na da nasaba da wani labarin ra’ayi mai taken “Ya Mai girma Gwamna Yusuf, ka kiyayi Kwamishinan Yada Labarai na Kano, Ibrahim Waiya,” wanda Auwal ya rubuta kuma aka buga a ranar 24 ga Fabrairu, 2025. Kungiyar ta yi tambaya kan dalilin da ya sa mawallafin kawai aka ware tare da mika shi wajen ‘yan sanda.
Kungiyar ta bayyana cewa an tsare Rano, editan jaridar Kano Times na tsawon sa’o’i a ranar 24 ga watan Maris a sashin binciken manyan laifuka (CIID) da ke rundunar ‘yan sandan Kano kafin a bayar da belinsa. Shi kuwa Auwal ‘yan sanda sun gayyace shi domin amsa tambayoyi a ranar 25 ga watan Maris.
Karin karatu: Gwamnatin Kano ta fara yunkurin saukaka rijistar masu kanana da matsakaitan sana’o’i
Gamayyar Kungiyoyin fararen hula, wacce ta hada da fitattun kungiyoyi da masu fafutuka sama da 40, ta yi gargadi kan yadda jami’an gwamnati ke amfani da jami’an tsaro wajen tursasa ‘yan jarida da masu fafutuka.
A cikin ‘yan shekarun nan, ‘yan jarida da masu fafutuka a fadin Najeriya na fuskantar kame ba bisa ka’ida ba, da tsare su ba bisa ka’ida ba, da kuma cin zarafi kawai saboda gudanar da aikinsu da kundin tsarin mulkin kasa ya ba su na sanar da jama’a,” a cewar wasikar.
Kungiyar ta jaddada cewa irin wadannan ayyuka sun sabawa sashe na 39 na kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda ya tabbatar da ‘yancin fadin albarkacin baki da ‘yan jarida, da kuma yarjejeniyoyin kare hakkin bil’adama na kasa da kasa da Najeriya ta amince da su.
Yana da matukar damuwa cewa jami’an gwamnati, maimakon a shiga tattaunawa ko ta shari’a, suna amfani da hukumomin tsaro na jihohi don murkushe muryoyin da ba su dace ba. Wannan cin zarafi ne da kuma yin barazana ga dimokuradiyya,” in ji Kwamared Bala Abdullahi Gaduwama, mai jagorantar kungiyar.
Kungiyoyin fararen hula sun yi kira ga kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano da ya tabbatar da cewa an biwa ‘yan jarida ‘yancinsu da kariyar doka.
Sun kuma bukaci gwamnatin jihar Kano da jami’an tsaro da su mutunta ‘yancin ‘yan jarida da kuma kaurace wa katsalandan da bai dace ba a harkokin jarida.
Kungiyar ta bayyana cewa ta kai rahoton lamarin ga kungiyoyin kare hakkin bil’adama na kasa da kasa, da suka hada da Amnesty International, Human Rights Watch, da kuma kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa (FIDH).
Kwamared Bala Abdullahi Gaduwama ne ya sanya wa wasiƙar hannu, kuma wasu fitattun mutane da suka haɗa da Dokta Y. Z. Ya’u (CITAD) da Comrade Auwalu Musa Rafsanjani (CISLAC) da Hajiya Amina Hanga (Isa Wali Empowerment Initiative) ne suka amince da takardar.
Wannan lamari ya kara nuna damuwa kan ‘yancin ‘yan jarida a Najeriya, yayin da ‘yan jarida ke ci gaba da fuskantar barazana da kuma tsangwama kan ayyukansu.













































