Babu tabbas ko zan tsaya takara a 2027 – Atiku

7fa03c25 1dac 4180 a74c 4fc5c5a8185b.jpg

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa babu tabbas ko zai tsaya takarar shugabancin ƙasar nan a zaɓen shekarar 2027.

Atiku ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da kafar talbijin ta Arise, wanda aka saki wani ɓangarenta a ranar Laraba.

An tambayi Atiku game da wanda zai jagoranci haɗakar da ƴan adawar ƙasar ke ƙoƙarin kafawa, sai Atiku ya ce tamkar abin da ya faru ne a lokacin da suka samar da jam’iyyar APC, inda bayan zaɓen fitar da gwani, dukkanin ƴan takarar suka mara wa mutum ɗaya baya, kuma ya yi nasara a babban zaɓen ƙasar.

Lokacin da aka tambaye shi ko zai yi takara, sai Atiku ya ce “ban sani ba, domin ya kamata ne a samar da kafa mai inganci tukuna.”

Karanta: Ƙudirin dokar cirewa mataimakin shugaban kasa da gwamnoni rigar kariya ya tsallake karatu na biyu

A makon da ya gabata ne Atiku Abubakar ya bayyana cewa ƴan adawa na ƙasar na tattaunawa domin yin haɗaka a ƙoƙarin tunkarar jam’iyya mai mulki a zaɓen Najeriya na 2027.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ne ya zo na biyu a zaɓen shugaban ƙasar na 2023, lokacin da Bola Tinubu ya samu nasara.

Sai dai tun bayan kama mulkin Tinubu al’ummar ƙasar na kokawa kan tashin farashin kayan masarufi da kuma tsadar rayuwa.

Masu lura da al’amuran yau da kullum a ƙasar na alaƙanta hakan da matakan da gwamnatin Tinubu ta ɗauka, kamar na cire tallafin man fetur da barin kasuwa ta tantance darajar kuɗin ƙasashen waje, abin da ya taimaka wajen karyewar darajar naira.

BBC

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here