Fassarawa: “`Aminu bala madobi“`
Ranar 29 Ga watan Mayun shekarar 2019, Ita ce ranar da a tarihi najeriya ba za a mance da ita ba, Wanda a ranar ne shugaba Muhammadu Buhari dan takarar jam’iyar APC ya lashe zabe a karo na biyu a matsayin shugaban kasa, bayan da ya sami adadin kuriu sama da Milyan 15 wanda hakan ya ba shi damar doke tsohon Mataimakin shugaban Kasa Atiku Abubakar Kuma dan takarar jam’iyar PDP da ya sami kuriu da suka doshi Milyan 11.
Wannan yanayi ba shi ne abu mafi jan hankali ba a ranar, face kafin wannan lokaci, an samu cukumurda iri iri da yan kunji kunji a kan batunnan da ya tada qura kan sahihancin runbun adana kuriun masu zabe da ya tada hazo a lokacin.
Ofishin yakin neman zaben SHUGABAN Kasa na Jam’iyar APC wanda kakakin sa a lokacin kwararren lauya, Festus Keyamo kê jagoranta wanda AYANZU Minista ne CIKIN kunshin fadar shugaban Kasa, ya sha kai korafe korafe ga jami’an tsaron farin kaya DSS kan cewa su binciki zargin da aka yiwa jagororin PDP da yunkurin yin kutse a runbunan adana kuriu na HUKUMAR Zabe.
Jam’iyar APC ta sha nuna yatsa tare da zargin PDP da hannu dumu dumu wajen yunkurin karan-tsaye ga wannan rumbu dan tunanin kokarin sauya lissafin manhajar na’urar tattara sakamakon zaben shugaban Kasa.
Wasu daga dandazon magoya bayan shugaba BUHARI sun doge matuka tare da yunkurin yin bore ga shugaba BUHARI yayin da yake kokarin rattaba hannu kan Dokar da ta bada damar aikewa da sakamakon zabuka kai tsaye a 2018 duk da cewa zabukan kakar 2019 a lokacin na dab da matsowa.
Wasu da dama a lokacin sun yi tunanin cewar hakan wata shiryayyen tuggu ne da jam’iyar hamayya ta PDP tayo na sauya fasalin kuriun zabe dan Kakaba Atiku Abubakar ko ta halin kaka.
Hakan kawai sai ya sani arashi, domin ba wani abune sabo gareni ba kasancewar tuni na saba da jin irin wadannan kulumboto da siddabarun siyasa wanda a cikin sauki ka Iya sauya tunanin me karamin tunani, ta haka zaisa su yi fatali da abu me amfani cikin rashin Sani, tambaya anan Ita ce shin siyasa a yanzu Wani mataki suka kai a Ilimi suka aminta da wancan yunkuri na yin gyara gyare ga kundin tsarin dokokin zabe kokuwa sun yi hakane da wata manufa dan yin aringizo ko zagon kasa ga BUHARI???
Wannan tunani na zuwar mini a wannan safiya lokacin da na karbi sakonni masu dama daga abokina, masoyi kuma gani_kashenin Atiku Abubakar
Mai taken YADDA AKA YAUDARI YA NAJERIYA.
Zuciya ta, ta farat daya sai ta kaini wani zaurancen Hausa dake cewa ” Wayon a ci ne aka kori kare daga bakin Dinya” Dinya sunan kalmar Hausa ce dake nufin bishiyar Dinya, Nyamurai na kiranta Uchakoeo Yayin da Yarbawa na kiranta Dori-nlu.
Hakika an zargi jam’iyar adawa da kokarin gurgunta tunanin masu zabe ta kowacce Irin fuska Misali zargin debo Yan Daba da tunanin shirin yin kulunboto iri iri dan goga kashin kaji tare da kokarin disashe farin jinin shugaba BUHARI.
Ga kadan daga irin wadannan sakonni da aka tattaro wasu mutane suka yi a shafukan jaridun kasar nan.
“Gwamnati me tunani zata iya kawo karshen matsalar wutar lantarki cikin watanni 6” Babatunde Raji fashola (Nov 12, 2014)
“Ku jefe mu( Mu Yan APC) idan ba mu yi muku komai ba cikin shekara 2” Tony Momoh (3 Aprilu 2016, Guardians ?Newspaper)
“Hanya Daya tilo ta samun dauwamammiyar wutar lantarki a najeriya ku Kori PDP” Babatunde Raji fashola (12 Yuli 2014, The Nation
“Lokaci ya yi da za asake gina najeriya: yanayin da ake ciki na gwamnati kê baiwa sassanta kason su daga asusun tarayya ya sanya jihohi kê kin yin katabus” Nasiër El rufai (Augusta 2010)
“Mafitakan halin da kasar nan ke ciki na kila_wa_kala shi ne majalisa ta mika kudiri na tsige shugaba Ummaru Musa Yaradua” Muhammad BUHARI, 10 Gawatan Maris 2010, Sun Newspaper)
“Me ze sa nafita waje neman lafiya ga asibitocin mu a gida bazamu gyara su a rika aiki ba” MUHAMMAD BUHARI Fabrairu 2015)
“Ta wanne dalili darajar Naira Ake Dillacin Kowacce $(dala1) a Nera 180” Babatunde Raji fashola 26 Gawatan Disamba 2014)
“Yanzu bari na baka misali akwai akalla Manyan Jirage 6 na shugaban Kasa, nawa Ake musu kasafi duk shekara dan kula da su, ba ma abatun kudaden tafiyar da su da sauran yan kace nace” Muhammad BUHARI Fabrairu 2015)
“Muna da niyyar farfado da tsarin sifirin jiragen saman Najeriya wato Nigerian Airways, zamu dawo da Jiragen fadar shugaban Kasa cikin tsarin Nigerian Airways, Kuma Zamu kara su zuwa 20 cikin shekara” (Muhammad BUHARI Fabrairu 2015)
A gefe guda, Duk da cewa bani da tabbaci kan sahihancin kalaman da aka rawaito Shugaba BUHARI Ya yi “Me ze sa na fita waje neman lafiya ga asibitocin namu a gida ba zamu gyara su rika aiki ba”
Zan iya cewa babu shakka APC karkashin shugaba BUHARI ta yi rawar gani kuma anga ci gaba bayyanne afannin môre rayuwa.
Masu kalubale ka Iya faden abun da suka ga dama amma Babu shakka BUHARI ya yi abubauwa muhimmai cikin dinbin manufofi, biyu daga ciki akwai fito da sabbin manufofi tare da tabbatar da su, Misali na farko ya yi nasarar kirkiro sabbin maaikatun tarayyar kuma a yau ake ganin alfanun su Misali Ma’aikatar kulada aikin yan sanda ta tarayya wadda Alh Muhammad Maigari Dingyadi kê jagoranta, se ma’aikatar jin Kai, tallafawa gajiyayyu da kare bala’o’i wadda uwargida Sadiya Umar Faruok kê jagoranta.
Duk da haka ma iya cewa izuwa yanzu abubuwa da dama sun damalmale sun dame, ta yadda kusan kowanne bigire kê neman karin ruwa domin da dama, turakun shakar numfashin kasar sun sukurkuce, kuma ire iren wadancan kalamai da jiga jigan siyasar suka yi a lokutan baya tamkar basu suka fada ba a yanzu.
Sai dai fa kar ku manta da zaurance na tun a karon farko wayon a cine….
Bala Ibrahim, Babban mashawarci kan yada labarai.












































