Jam’iyyar APC za ta bayyana sabuwar ranar sayar da fom ɗin takara

APC Convention
APC Convention

Masu neman tsayawa takarar mukamai a zaɓen baɗi a ƙarƙashin jam’iyyar APC, za su ɗan jira kafin su sayi fom ɗin na-gani-ina so.

Solacebase ta ruwaito cewa an shirya fara sayar da fom ɗin ne yau Asabar, amma ziyarar sakatariyar jam’iyyar ta nuna jinkirin fara sayarwar.

Wata majiya mai tushe a sakatariyar jam’iyyar ta shaida wa Kamfanin dillancin Labarai na Najeriya NAN cewa, masu buga foma-foman ne ba su kai su ba har lokacin tashi daga shalkwatar jam’iyyar ranar Juma’a.

Majiyar ta tabbatar da cewa, za a fara sayar da fom ɗin nan ba da jimawa ba bayan an kai kayan aikin sakatariyar.

“Sauya tsarin ya faru ne saboda ɗan kwangilar bai kawo fom ɗin ba a lokacin da ake gab da kammala aiki ranar Juma’a, amma yana iya bayarwa kafin ƙarewar ƙarshen mako.

“Idan hakan ta faru, ana iya fara sayar da fom a ranar Litinin ko Talata.

“Kwamitin ayyuka na jam’iyyar na ƙasa ne zai tantance sabuwar ranar,” inji majiyar.
Sakataren yaɗa Labaran jam’iyyar na ƙasa Mista Felix Morka, bai mayar da martani ga sakonnin da aka yi masa ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here