Da Dumi-Dumi: Gobara ta hana zirga-zirga a filin jirgin saman Legas

Gobara, legas, filin, jirgin, saman
Wata gobara da ta tashi a safiyar ranar Alhamis ta kawo cikas ga aikin jirgi a filin jirgin Murtala Muhammed da ke Legas. Da take tabbatar da faruwar...

Wata gobara da ta tashi a safiyar ranar Alhamis ta kawo cikas ga aikin jirgi a filin jirgin Murtala Muhammed da ke Legas.

Da ta ke tabbatar da faruwar lamarin, hukumar kula da filayen jiragen sama ta tarayyar Najeriya FAAN a wata sanarwa da daraktan hulda da jama’a da masu sayayyar kayayyaki, Obiageli Orah ya fitar, ta ce gobarar da ta barke ta haifar da karkatar da dukkan ayyukan jirgin daga tasha 1 na tashar jirgin zuwa tashar jirgin D wing.

Karin labari: Fursunoni sama da 100 sun tsere a jihar Neja a dalilin barkewar ruwan sama

A cewar Orah, injiniyoyin da ke filin jirgin sun katse wutar lantarki daga dukkan reshen E na filin jirgin a kokarin da suke na kashe wutar.

Orah, wanda ya bayyana cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 5:29 na safe, ta ce hayakin da ya rikide ya zama wuta ya tashi daga gadar E54.

Orah ya ce, “An gano hayaki yana ta turnukewa daga gadar E54, wanda hakan ya sa injiniyoyin lantarki suka katse wutar lantarki ga daukacin E Wing.

Karin labari: Kungiyar CHRICED ta yi Allah-wadai da zargin kariyar da Gwamna Ododo ke ba Yahaya Bello

“Rundunar ceto ta filin jirgin sama da masu kashe gobara (ARFFS) sun yi gaggawar mayar da martani, inda suka isa wurin da karfe 05:30 na safe. Abu na farko na nuni da tartsatsin wuta daga na’urar lantarki a matsayin musabbabin, amma ana ci gaba da gudanar da cikakken bincike don gano musabbabin tashin gobarar.

“Al’amarin wanda ya rikide zuwa gobara, an shawo kan lamarin da karfe 06:41 na safe. Ana ci gaba da kokarin kawar da hayakin ginin.

Karin labari: Hukumar FAAN ta sake bude titin jirgin sama bayan hatsarin jirgin Dana

“A halin yanzu, duk ayyukan jirgin a Terminal 1 na MMA an karkatar da su zuwa D Wing. Karin bayani zai biyo baya nan ba da jimawa ba.”

An bayyana cewa lamarin ya haifar da tashin hankali da firgici a filin jirgin, lamarin da ya tilastawa wasu jami’an filin jirgin da matafiya yin tururuwa zuwa inda suke.

Sai dai tawagar FAAN da hukumar ceto da kashe gobara ta filin jirgin sun dawo da zaman lafiya a filin jirgin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here