Kungiyar (CHRICED) ta kasa ta yi Allah-wadai da matakin da Gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo ya dauka, kan zargin rigar kariya ga tsohon Gwamnan jihar Yahaya Bello daga kama shi.
Kungiyar a cikin wata sanarwa da babban daraktan ta, Ibrahim M. Zikirullahi, ya fitar, ta ce ta bi diddigin abubuwan da suka wakana, tun bayan yunkurin da hukumar EFCC ta yi a kwanan baya na cafke Bello bisa zargin tuhume-tuhume 19 da karkatar da Naira Biliyan 84.
Karin labari: Gwamna Zulum ya amince da nadin mukaddashin shugaban jami’ar Borno
Sai dai kungiyar CHRICED ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya dauki kwakkwaran mataki kan cin hanci da rashawa, “Muna kira ga Shugaban kasa da ya ba Gwamna Ododo wa’adi, inda ya bukaci Yahaya Bello ya mika wuya ga EFCC. Rashin yin biyayya ya kamata a sanya dokar ta baci a jihar Kogi” in ji sanarwar.
“Sanarwar ta bakin Zikirullahi ta kara da cewa, “Za mu iya daukar darasi daga kasashe irin na Larabawa da China, inda aiwatar da tsauraran hukunce-hukunce shi ne abinda ya kamata.”
Karin labari: Hukumar FAAN ta sake bude titin jirgin sama bayan hatsarin jirgin Dana
“Wadannan kasashe sun nuna cewa rashin hakuri da sata na iya dakile irin wadannan laifuka yadda ya kamata,” in ji kungiyar.