Kungiyar likitoci da na hakora ta Najeriya (MDCAN) ta bayar da wa’adin kwanaki 21 ga gwamnatin tarayya da ta aiwatar da bita domin duba tsarin albashin likitocin (CONMESS) da sauran bukatun su.
Hakan na kunshe a cikin wata sanarwar da aka fitar ranar Litinin bayan kammala taron majalisar zartarwa ta kasa na kungiyar.
Sanarwar ta samu sa hannun shugaban kungiyar, Victor Makanjuola, da Sakatare Janar na kungiyar, Yemi Raji.
Kungiyar ta ce tana takaicin, rashin aiwatar da yarjejeniyar hadin gwiwa da aka amince da ita na CONMESS da kuma bullo da alawus alawus da kungiyar likitocin Najeriya (NMA).