Ana zanga-zangar ƙyamar cin hanci a kotunan zaɓe na Kano

IMG 20230821 WA0006 750x430
IMG 20230821 WA0006 750x430

Wasu kungiyoyin fararen hula a Kano sun gudanar da zanga-zangar nuna kyamar zarge-zargen cin hanci da rashawa da ya dabaibaye kotunan sauraren kararrakin zabe.

A makon da ya gabata ne taƙaddama da ɓarke, bayan Mai shari’a Flora Ngozi Azinge, shugabar kotun sauraron ƙorafin zaɓen ‘yan majalisun tarayya da na jihar Kano, ta sake fitowa ta koka game da yunƙurin bai wa alƙalan kotun cin hanci da nufin tauye adalci.

Rahotanni dai sun ambato Mai shari’a Flora Azinge na cewa karo na biyu ke nan wani alƙalin kotun na kai mata ƙorafi a kan yadda wasu lauyoyi da ke cikin ƙararrakin da kotun ke sauraro, suna ƙoƙarin ba su cin hanci.
Manyan jam’iyyun siyasar jihar guda biyu NNPP mai mulki da APC, babbar mai hamayya a Kano suna nuna wa juna yatsa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here