‘Yan Jarida 56 aka Garkame a Gidan Yari A Nahiyar Africa a 2022

journalists sabo
journalists sabo

‘Yan jarida da dama ne ke daure a gidajen yari a fadin Nahiyar Africa sakamakon aikata wasu laifuka masu yawa.

Wani rahoto da Kwamitin Kare ‘Yan Jaridu ya fitar ya nuna cewa an hana ‘yan jaridu 363 ‘yancinsu na aiwatar da ayyukan su daga ranar 1 ga Disamba, 2022 a matsayin wanda ya zarce na bara da kashi 20%.

Rahoton ya ce akalla ‘yan jarida 56 ne aka daure a gidajen yari a fadin Afirka a shekarar 2022 inda Masar ta kasance kan gaba.

“Masar ta ci gaba da kasancewa kan gaba wajen tsare ‘yan jarida a fadin Afirka, duk da cewa an sako wasu daga kasashen duniya.

Kasar Eritriya na ɗaya daga cikin ƙasashen da aka fi sanyawa ‘yan jaridu takunkumi a duniya. Mafi akasarin ‘yan jaridar da ake tsare da su a gidan yari an tsare su ne ba tare da an gurfanar da su a gaban kotu ba tsawon shekaru 21,” inji rahoton.

“Kasar Kamaru wadda a halin yanzu ake tsare da wasu ‘yan jarida tun a shekarar 2016. Kasar Senegal na daure wani dan jarida daya a gidan yari saboda aikinsa, Pape Alé Niang, wanda shi ne karon farko da kasar da aka tsare tun shekara ta 2008.

“Uku daga cikin ‘yan jarida 4 da aka daure a Ruwanda masu amfani da kafar YouTubes ne. Biyu daga cikinsu – Aimable Karasira da Dieudonné Niyonsenga sun yi zargin cewa an azabtar da su da kuma wulakanta su yayin da suke tsare.

“Dan jaridar Faransa Olivier Dubois, wanda aka sace a Mali a watan Afrilun 2021, da wasu ‘yan jaridar Tigrai TV guda biyar, da ake tsare da su a garin Mekelle da ke arewacin kasar Habasha, ba a saka su cikin adadin jama’ar ba saboda suna hannun wadanda ba na gwamnati ba.”

An kashe ‘yan jarida 24 da ma’aikatan yada labarai a Najeriya tsakanin shekarar 1992 zuwa 2022.

A ranar 13 ga Oktoba, 2022, jami’an ‘yan sanda sun tsare Abdulrasheed Akogun tare da dan uwansa Dare Akogun kan zargin aikata laifuka kan kalaman da suka wallafa a wata kungiya ta WhatsApp.

Ana zargin ‘yan jaridar ne da laifin hada baki, bata suna, tada tarzoma da kuma yin amfani da yanar gizo kan zargin cewa Rafiyu Ajakaye, babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar Kwara, ya yi rub-da-cikin wasu kudade akokarin sauya sakamakon zabe.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here