Shugaban kasa Muhammad Buhari ya ce ya yi iya kokarinsa ga ‘yan Najeriya duk da tabarbarewar tattalin arziki da rashin tsaro.
Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake maraba da babban sakataren kungiyar Abu Dhabi, Sheikh Al-Mahfoudh Bin Bayyah da mataimakinsa Fasto Bob Roberts na kasar Amurka, wadanda suka ziyarce shi a birnin Washington.
Cikin wata sanarwa da Garba shehu ya fitar, ya lura cewa aikin da suke yi na inganta tattaunawa tsakanin addinai daban-daban yana da mahimmanci ga duniya kamar yadda yake da mahimmanci ga Najeriya.
“Ayyukan ku na da matukar muhimmanci wajen taimakawa, musamman matasa, su fahimci juna, kuma a lokaci guda, su yi alfahari da al’adun su,” in ji Mista Buhari.
Shugaba Buhari yace gwamnatinsa na kokari wajan fuskantar kalubale da dama, amma a fannoni da dama, muna kokari. A cikin shekaru bakwai da rabi, na yi iya kokarina.”
Babban sakataren ya ce sun zo ne domin sanar da shugaban kasar da kuma gayyatarsa da ya halarci bikin karramawar da gidauniyar Abu Dhabi ta ba shi, saboda irin nasarorin da ya samu wajen inganta zaman lafiya da tsaro.













































