Gwamnatin Jihar Kano ta bawa masu buqata ta musamman damar karo karatu a kasashen ketare.

AKY 47
AKY 47

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa masu buqata ta musamman damar karo karatu a kasashen ketare.

Alhaji Umar Haruna Doguwa, kwamishinan ilimi na Jihar ya bayyana hakan a wata sanarwa, in da yake cewa “A cikin masu buqata ta musamman duk wanda yake da cikakkun takardun da ake nema, yana da dama cin wannan gajiya da gwamnatin kano ta farfado da shi.”

Jawaban na kunshe a cikin wata sanarwa da ta fito daga ma’aikatar ta hannun Ameen K. Yassar, Daraktan wayar da kan al’umma.

“Zamu tabbatar da mun bawa masu kwalin digiri ajin farko da na biyu, zamu kuma shigar da masu buqata ta musamman a cikin masu cin gajiyar wannan tallafin, yin hakan zai zama basu kwarin guiwa domin zama mutane na kwarai a cikin al’umma.” jaridar SOLACEBASE ce ta rawaitpo hakan a cikin jawabin Doguwa a lokacin da yake tattaunawa da wakilan Mercy corps, Hadakar qungiyoyin masu buqata ta musamman ta sauran qungiyoyi masu zaman kansu a ranar laraba a ofishin sa.

Kwamishinan ya bada tabbacin gwamnatin Jihar na da kyakyawar niyya akan aiki da qungiyoyi masu zaman kansu, domin kawo cigaba da mutanen jihar zasu amfana.

Haka zalika, wakiliyar Mercy Corps, Nafisa Amadu Abubakar, da sauran wakilan masu buqata ta musamman, da sauran kungiyoyi sun yi kira ga gwamnatin jihar, ta hada taron wayar da kan al’umma, domin jawo masu buqatar a jiki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here