Jami’an hukumar Hisbah a jihar Krabbe, wadda ke karkashin Ma’aikatar Harkokin Addini ta jihar Kebbi, sun kama wani mutum da aka same shi a boye a cikin jakar “Ghana Must-Go” a gidan matar aure da ke yankin Badariya a Birnin Kebbi.
Daraktan Shari’arhukumar, Sirajo Kamba, ya tabbatar da kama mutumin a cikin wata sanarwa da ya fitar ga Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) a ranar Talata a Birnin Kebbi.
A cewar Kamba, mazauna yankin sun sanar da Hisbah da misalin karfe 12:15 na daren Litinin, 18 ga Mayu, bayan sun lura da wani mutum na shiga gidan matar.
“Mazauna yankin sun yi zargin haramtacciya alaka da ta saba wa koyarwar Musulunci, saboda haka suka yanke shawarar sanar da hukuma bisa ka’ida.
“Bayan karbar rahoton, Hukumar Hisbar nan da nan ta tura jami’ai don gudanar da bincike.
“Da jami’an suka isa, sun nemi izinin binciken gidan amma matar da farko ta musanta cewa akwai wani a ciki,” in ji shi.
Sai dai daraktan ya ce daga baya matar ta amince kuma ta ba da izinin yin bincike, wanda hakan ya kai ga gano wanda ake zargin a boye a cikin jakar ‘Ghana Must-Go’.
Ya kara da cewa bayan gudanar da bincike, ya nuna ana zargin akwai alaka ta soyayya tsakanin mutumin da matar aure.
Kamba ya ce bayan tambayoyi, masoyan biyu sun amince da zargin, inda ya kara da cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu domin fuskantar shari’a bisa dokar Musulunci.
(NAN)












































