ADC ta tantance sama da ‘yan takarar Gwamna 70 gabanin zaben fidda gwani

ADC ADC 750x430

Jam’iyyar ADC ta ce ta tantance sama da ‘yan takarar Gwamna 70 a ranar farko ta aikin tantancewa gabanin zaben fidda gwanin jam’iyyar.

Mataimakiyar Sakataren Yada Labarai Jam’iyyar na Kasa, Misis Queen Okiyi, ce ta bayyana hakan yayin da take wa manema labarai bayani a ranar Litinin a Abuja.

Okiyi ta ce aikin ya gudana cikin nasara, inda kwamitocin tantancewa guda biyu suka kula da ‘yan takara 35 kowannensu.

Ta kara da cewa sama da ‘yan takarar Gwamna 100 daga jihohin da za a gudanar da zaben ne ke halartar aikin.

A cewarta, tantancewar za ta ci gaba a ranar Talata yayin da jam’iyyar ke ci gaba da tantance karin ‘yan takara.

Ta ce aikin yana nuna kudurin jam’iyyar na bin ka’ida da zabar ‘yan takara masu inganci.

“Kawo yanzu, an tantancewar ta kare a yau, kuma za ta ci gaba gobe,” in ji Okiyi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN), ya ruwaito cewa ADC ta tsara tantance ‘yan takarar Shugaban Kasa ranar Laraba, 20 ga Mayu.

NAN ta kuma ruwaito cewa tantance ‘yan takarar Majalisar Tarayya da abin da ya shafa daga wasu sassa na Arewacin Najeriya yanzu za a gudanar da ita a Abuja saboda dalilan tsaro. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here