Shugaba Buhari ya yi Allah-wadai da kisan Kwamishinan Katsina

Buhari speaks
Buhari speaks

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya yi Allah-wadai da kashe kwamishinan kimiyya da fasaha na jihar Katsina, Dakta Rabe Nasir da aka yi a yammacin ranar Alhamis.

Shugaban a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Malam Garba Shehu ya fitar a yammacin ranar Alhamis, ya bayyana kisan kwamishinan a matsayin wani mummunan aiki tare da yin Allah wadai da shi, inda ya kara da cewa “babu inda za a yi irin wannan tashin hankali a kasarmu.”

Shugaban ya ce ya ji takaicin kisan gillar da aka yi wa wannan gwarzon ma’aikaci wanda ya yi wa al’ummarsa da jiharsa da ƙasa hidima da kwazonsa.

“Tunanina yana tare da danginsa bisa wannan babban rashi.” in ji shugaban.

Ya bukaci jami’an tsaro da su yi cikakken bincike tare da gurfanar da waɗanda ke da hannu wajen aikata laifin.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here