Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da sauye-sauyen kananan mukamai a majalisar zartarwa tare da sake tura manyan jami’an gwamnati a ma’aikatu daban-daban.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, ya fitar, inda ya bayyana cewa matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin inganta shugabanci da kuma ƙara ingancin ayyukan gwamnati a fannoni daban-daban.
A cewar sanarwar, kwamishinan shari’a kuma babban lauyan jihar, Barista Haruna Isa Dederi, an tura shi zuwa ma’aikatar sufuri.
Haka kuma, babban sakatare na ma’aikatar, Barista Mustapha Nuruddeen Muhammad, an maida shi zuwa ma’aikatar muhalli a matsayin sabon babban sakatare.
Kwamishinan kula da harkokin jin kai, wanda ke rike da mukamin kwamishinan sufuri na rikon kwarya, zai koma ma’aikatarsa ta asali ta harkokin jin kai.
An umarci dukkan jami’an da sauye-sauyen suka shafa da su mika ragamar ofisoshinsu ga jami’in da ya fi kowa girma a ma’aikatar.
Gwamna Yusuf ya bukaci a kammala aikin miƙawa da karɓar ragamar mulki daga ranar Talata 23 ga Satumba, 2025, kafin ƙarshen lokacin aiki.
Ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da mutunta gaskiya, inganci da shugabanci mai ma’ana.
Gwamnan ya bayyana cewa sake tura jami’an gwamnati zai taimaka wajen amfani da basirar kowanne, daidaita nauyin aiki da kuma tabbatar da cewa gwamnati tana isar da sakamakon da ake bukata ga al’ummar Kano.
Ya kuma bukaci jami’an gwamnati da su bai wa sabbin kwamishinoni haɗin kai domin su gudanar da aikinsu yadda ya kamata.













































