Wani marubuci daga Kano, Malam Iliyasu Mu’azu Sharada, ya sha alwashin gurfanar da gidan GCMX Radio Talabijin a gaban kotu bisa zargin karya haƙƙin mallakar littafinsa mai suna “Kamus Na Kayan Sarautar Kasar Hausa”.
Sharada, wanda kuma shi ne dagacin Sharada, ya shaida wa jaridar SolaceBase a daren Litinin cewa ya ɗauki matakin shigar da ƙara saboda an tauye masa haƙƙin mallakar fasaha.
Ya bayyana cewa a ranar 21 ga Agusta, 2025, wani shirin gidan rediyon mai suna “Kowa Ya Raina Mafari Zai Rasa Tabarmarsa” ya tattauna kai tsaye kan littafinsa.
A cewarsa, shirin wanda ake watsawa duk Alhamis da ƙarfe 7:30 na safe tare da maimaitawa Talata da ƙarfe 9:00 na safe, ya karanta abubuwa daga littafinsa “kalma da kalma” ba tare da an ambaci shi a matsayin marubuci ba.
Karin labari: Kotu ta umarci sake buɗe makarantar Sakandaren Prime College a Kano
Ya ce kalmomi kamar Bundiga da Takalmi sun fito daga rubutunsa kai tsaye.
Lauyoyinsa sun aike da takardar korafi ga hukumar gidan rediyon, inda suka bayyana lamarin a matsayin “tauye haƙƙin mallakar fasaha” da ya sabawa dokar kare haƙƙin mallaka ta ƙasa.
Sun bukaci biyan diyyar naira miliyan 20 tare da wa’adin makonni biyu domin sasanta matsalar.
Sai dai a martanin da lauyoyin GCMX suka aiko a ranar 30 ga Agusta, 2025, sun musanta duk wata alaka da littafin Sharada, tare da cewa ba su taɓa ganin ko karanta shi ba.
Wannan ya sa rikicin ya ƙara tsananta, inda Sharada ya dage kan cewa zai bi ta kotu domin neman adalci, yayin da gidan rediyon ya tsaya kan matsayinsa na rashin laifi.













































