Dantakarar gwamna a jihar Kano a karakashin jam’iyyar (ADP), kuma dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Municipal a majalisar tarrayar Najeriya, Sha’aban Ibrahim Sharada, ya kalubalanci gwamnatin Kano bisa sa dokar hana ‘yan adaidaita sahu bin wasu manyan titunan jihar, batare da gudanar da isheshshir tuntubar masana da kuma musa ruwa da tsaki ba.
Sha’aban Ibrahim Sharada ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa, Abbas Yushau Yusuf, ya rabawa manema labarai ranar Laraba a Kano.
Sanarwar ta ce a lokacin da ya kamata gwamnati ta fitu da hanyoyi da dabaru domin dauke hankalin matasa daga shaye-shaye, da kuma aikata muggan laifika a jihar, sai gwamnatin ta buge da kawo tsarin da zai kara tun zura matasan.
Sanarwar ta kara da cewa gwamnatin kwamata yai tayi duk mai yuwuwa wajan habbaka tattalin arzakin masu sanar adai-dai-ta sahun, ba wai ruguzasu ba.
Sha’aban Ibrahim Sharada ya yi kira ga jama’ar Kano da su zabe shi a kakar zabe mai zuwa, domin kawo gwamnatin da zata tafi da a’umma yayin yanke duk wani hukunci.










































