Wani da ake zargin dan damfara ne ya mika kansa ga EFCC

EFCC EFCC Sabo

A ranar Litinin da ta gabata ne wani da ake zargi da damfarar mutane a fannin daukar aikin yi, Idris Adamu, ya mika kansa ga hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC a jihar Gombe bisa zarginsa da aikata laifin da ake zarginsa ta hanyar karya.

jami’inhulda da jama’a na hukumar ta EFCC, Dele Oyewale ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja.

Oyewale ya bayyana cewa an yi wani abu mai kama da almara a shalkwatar hukumar EFCC na shiyyar Gombe, lokacin da matashin mai matsakaicin shekaru ya shiga harabar ofishin ya kai karar kan tare da bayyana irin laifukan da ya ke aikatawa na zambatar mutane.

Ya ce wanda ake zargin da kan sa ya bayyana cewa yana tsoron hukumar ta EFCC ne saboda irin laifukan da ya ke aikatawa.

“Wanda ake zargin, Idris Adamu, ya shiga ofishin EFCC ne da misalin karfe 1:00 na rana, ya kuma bukaci ganin shugaban riko na shiyyar ko kuma mataimakin kwamandan EFCC DCE, Sa’ad Hanafi Sa’ad.
“Ya ce yana so ya fadi wasu boyayyun bayanan gaskiya game da laifukan da ya aikata a baya,” in ji shi.

A cewarsa, a lokacin da yake ofishin Daraktocin, wanda ake zargin ya ce, “Na zo ne domin in tuba daga laifuffukana da kuma shaida wa EFCC.

“A baya na samu jimillar kudi naira miliyan 9 ta asusun ajiyana na banki daga wasu mutane daban-daban da sunan sama musu aikin yi a ma’aikatun gwamnatin tarayya wanda karya na shirya musu.
“Na canza amma ina tsoron EFCC,” in ji wanda ake zargin.

Oyewale ya ce, mukaddashin daraktan shiyyar bayan ya saurari furucin nasa, ya gode masa da yin wannan tuba.

A cewar sa, Sa’ad saboda haka ya bayar da umarnin a kai wanda ake zargi da kansa zuwa sashin bincike domin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here