Rundunar sojin kasar Saudiyya ta tura jami’an tsaro sama da 40,000 domin bayar da tsaro a wuraren da za a gudanar da ibadar aikin Hajjin bana.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, ana jibge jami’an tsaro a wasu muhimman wuraren ibada da suka hada da Makkah da Mina da Arafat da Muzdalifah.
Daraktan tsaron Jama’a kuma shugaban kwamitin tsaron Alhazai Laftanar-Janar Mohammed Al-Bassami, shi ne ya tabbatar da hakan ya na mai cewa kare lafiyar alhazai ya kasance abu mafi fifiko a garesu.
Da yake jawabi a wajen wani gagarumin fareti da atisayen soji da aka yi a Makkah, gabanin fara bayar da aikin tsaron a Hajjin bana, Al-Bassami ya ce, aikin tsaron muhimmin abu ne ne.
Ministan cikin gida na kasar, Yarima Abdulaziz bin Saud, shi ma ya jagoranci atisayen soji da jami’an tsaron Hajji suka gudanar, wanda ya hada da baje kolin da suka hada da dakaru, da jirage masu saukar ungulu, da tarin kayan aikin soji.
NAN ta ruwaito cewa an gudanar da atisayen ne da nufin nuna shirye-shirye gudanar da ayyukan jami’an tsaro da ke da alhakin kula da aikin hajjin na bana.
A yayin atisayen dai jami’an tsaro sun yi jerin gwano yayin da runduna ta musamman da suka hada da kwamandojin kasar suka gudanar da baje-kolin irin kwarewa da dabarun ayyukansu, wanda ke nuna cikakken tsarin tsaro na aikin Hajji.













































