Bankin duniya makiyin Najeriya ne-Kungiyar Kwadago

NLC President Joe Ajaero and the World Bank logo
NLC President Joe Ajaero and the World Bank logo

Kungiyar Kwadago ta kasa NLC ta bayyana bankin duniya a matsayin makiyin Najeriya.

NLC ta bayyana hakan ne bayan da Bankin ya bukaci gwamnatin tarayya dakatar da biyan tallafin mai tare da kara farashin man zuwa Naira 750 kan kowacce lita.

Ta caccaki babban masanin tattalin arziki na Bankin a Najeriya, Alex Sienaert, saboda goyon bayan shawarar da ba ta dace ba.

Bankin Duniya
Bankin Duniya

Karanta wannan: Gwamnonin jihohin Arewa suna taro a Kaduna

Yayin da take zargin bankin da inganta manufofin dake kare muradan kasashen waje fiye da al’ummar Najeriya.

Kungiyar ta shawarci gwamnati da ta yi watsi da tasirin kasashen waje a tsare-tsaren tattalin arziki tare da fifita jin dadin al’ummarta.

NLC ta kuma yi kira ga gwamnati da ta yi amfani da albarkatun cikin gida don magance matsayin rayuwa ga ‘yan Najeriya.

Kungiyar ta kuma gargadi Bankin Duniya da ya kaucewa tsoma baki a harkokin tattalin arzikin Najeriya.

Ya kuma baiwa kasar damar aiwatar da manufofinta da za su amfani ‘yan kasa a tsawon shekaru da dama.

A baya-bayan nan dai Bankin ya shawarci gwamnati tarayya da ta daina biyan kudin tallafin man fetur.

Yayin da kuma ya yi hasashen cewa farashin man ka iya zama Naira 750 kan ko wacce lita.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here