Hukumar NDLEA ta kama wanda ake zargi da kashe jami’inta a Sokoto

NDLEA
NDLEA

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA ta kama mutane 59

bisa zargin safarar miyagun kwayoyi a Sokoto.

NDLEA ta kuma kama wanda ake zargi da hannu wajen kashe jami’in ta.

Hukumar NDLEA
Hukumar NDLEA

Kwamandan NDLEA a jihar, Muhammad Iro, ne ya bayyana hakan ranar juma’a.

Yace wanda ake zargin, da ba a bayyana sunan sa ba, an kama shi ne tun a watan Janairu a Bagarawa da ke karamar hukumar Bodinga.

Karanta wannan: Gwamnonin jihohin Arewa suna taro a Kaduna

Iro ya bayyana takaicinsa kan kin tallafawa hukumar da al’umma ke yi.

Ya kuma jaddada bukatar dake akwai cewa jama’a su san nauyin da ke wuyansu.

Ya ce wanda ake zargin na cikin jerin sunayen da NDLEA da ‘yan sanda ke nema ruwa a jallo.

Iro ya ba da tabbacin cewa wanda ake zargin zai fuskanci hukunci kuma za a gudanar da bincike don gano wadanda ke da hannu a ciki.

Karanta wannan: Bankin duniya makiyin Najeriya ne-Kungiyar Kwadago

A cewarsa, za a gudanar da bincike a kan wadanda ake zargin domin gurfanar da su gaban kuliya.

Iro ya ce hukumar su ta himmatu wajen kawar da miyagun laifuka tare da wayar da kan jama’a game da illolinsu.

Ya kuma bukaci al’umma da su rinka taimakawa NDLEA da bayanan sirri kan wuraren da ake sha ko fataucin miyagun kwayoyi.

A baya-bayan nan dai NDLEA ta tarwatsa wani taron angwanci da ake yin gasar shan miyagun kwayoyi a Jihar Katsina.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here