Yayin da ya ‘yan kwanaki a fara gudanar da bikin babbar Sallah, masu sayar da raguna a Kasuwar Dabbobi ta kasa da kasa ta Mai’adua da ke jihar Katsina sun koka da yadda ake samun karancin abinci da kuma dabbobi.
Wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN da ya ziyarci kasuwar a ranar Lahadin da ta gabata, ya ruwaito cewa, korafin dillalan dabbobin ya biyo bayan hana fitar da dabbobi da hukumomin sojin Jamhuriyar Nijar suka yi zuwa Najeriya.
NAN ta ruwaito cewa hakan na faruwa ne duk da matakan da gwamnatin tarayya ta dauka na saukaka kasuwanci tsakanin kasashen biyu.
Irin wannan kokari dai ya hada da aikin layin dogo na biliyoyin daloli daga Kano ya bi ta Jigawa da Katsina zuwa birnibn Maradi na jamhuriyar Nijar, wanda shugaba Bola Tinubu ya bayyana kwanan nan a Katsina, wanda za a kammala shi a shekarar 2026.
A halin da ake ciki kuma, an gano wani katon rago wanda ya kai Naira miliyan 1 da dubu dari 7 da na Naira miliyan 1 da dubu dari 2, yayin da aka sayar da wani matsakaicin rago kan Naira 700,000 yayin da farashin kananan raguna ya fara daga Naira 100,000.
Bashir Hassan, wani dillalin raguna ne daga Jamhuriyar Nijar, ya ce hukumomi sun ba da umarnin cewa ba za a bar kowa ya fita da rakuma ko shanu ko raguna ko akuya ba.
Ya kara da cewa, umarnin ya biyo bayan ambaliyar ruwa da aka samu a shekarar 2024 a Niamy da Maradi da Tawa da sauran wasu yankuna inda hakan ya yi sanadiyyar kashe dabbobi da dama.
Hassan ya bayyana cewa an umurci jami’an ‘yan sanda da na shige da fice da sojoji da kuma sarakunan gargajiya da su kwace dabbobi daga hannun duk wanda ya yi yunkurin tsallakewa da su.
Ya ce an kama dabbobi da dama daga hannun wadanda suka yi yunkurin tsallaka kan iyakar kasar, lamarin da ya haifar da karancin abinci, duk da cewa tallafin da ake samu ya yi kadan, idan aka kwatanta da shekarar 2024.
Sai dai wani dillalin mai suna Alhaji Mu’azu Maifaru ya bayyana cewa wannan umarni ya fi shafar mutane daga Jamhuriyar Nijar, inda ya ce “amma ga matsalar tsaro a wasu yankunan Najeriya na da manya-manyan gonaki da za su iya samar da isassun dabbobi har ma da fitar da su zuwa kasashen waje.













































