Gwamnatin jihar Kano ta amince da kashe Naira biliyan 19.02 domin aiwatar da muhimman ayyukan ci gaba a fannoni daban-daban na tattalin arzikin jihar.
Amincewar ta biyo bayan taron majalisar zartarwa karo na 33 da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar ranar Asabar, karkashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf.
A cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar, an bayyana cewa kudaden za su shafi fannoni kamar ilimi, kiwon lafiya, hanyoyi da gine-gine, samar da ruwa da kuma ci gaban makamashi.
Fannin ilimi zai karɓi Naira biliyan 4.93 domin gyaran makarantun gwamnati, biyan basussukan abincin ɗalibai makarantun kwana da tabbatar da izinin gudanar da karatu a manyan makarantu.
Daga cikin muhimman ayyuka akwai na Naira biliyan 2.54 domin gyaran kwalejin fasaha ta gwamnati da ke Ungogo, da kuma Naira miliyan 400 na kujeru a jami’ar NorthWest.
Fannin kiwon lafiya zai karɓi Naira miliyan 274 domin gyaran asibitin Tiga da asibitin yara na Hasiya Bayero, yayin da fannin albarkatun ruwa zai samu Naira biliyan 3.34 domin biyan kudin makamashi, man fetur da kuma gina sabon matatar ruwa a Rano.
Ma’aikatar ayyuka da gine-gine za ta karɓi Naira biliyan 9.85 domin gina manyan hanyoyi, gyaran wuraren ambaliyar ruwa, da kuma saka fitilun titi da na zirga-zirga masu amfani da hasken rana a fadin jihar.
Domin ƙarfafa samar da makamashi mai ɗorewa, gwamnati ta amince da Naira miliyan 979 domin shigar da hasken rana a ginin Africa House da kuma ofishin kula da harkokin majalisar.
Haka kuma majalisar ta amince da Naira miliyan 586 domin gina wuraren auna nauyin motoci a Doguwa da wasu manyan ƙofofin shiga jihar, da kuma Naira miliyan 149 domin shirye-shiryen aikin Hajjin shekara ta 2026.
Sanarwar ta tabbatar da cewa gwamnatin jihar Kano za ta ci gaba da gudanar da mulki bisa gaskiya, adalci da kuma ɗorewar kyautata rayuwar al’umma.












































