Da ɗumi-ɗumi: Ƴan sanda sun cafke mutane 3 da ake zargi da kisan Uwar da yara 6 a Kano

WhatsApp Image 2026 01 18 at 10.44.11 750x430

Rundunar ƴan sandan Jihar Kano ta cafke mutane uku da ake zargin suna gaba gaba wajen da hannu a kisan gilla da aka yi wa wata matar aure da ’ya’yanta shida a unguwar Dorayi Chiranchi da ke cikin birnin Kano.

Sanarwar cafke mutanen ta fito ne daga kakakin rundunar ƴan sandan Jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, a ranar Lahadi, inda ya bayyana matakan tsaro da aka ɗauka domin dakile laifuka masu tsanani a jihar.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa cafke mutanen ya biyo bayan wani shiri na bayanan sirri da Sufeton ƴan sandan ƙasa, Kayode Adeolu Egbetokun, ya bayar da umarni a kansa, tare da jagorancin Kwamishinan ƴan sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori.

An aiwatar da aikin ne ta hannun ƙungiyar masu bincike tsakanin ƙarfe 10:00 na dare a ranar 17 ga Janairu zuwa ƙarfe 4:00 na asuba a ranar 18 ga Janairu, 2026, a wasu sassan birnin Kano.

Labari mai alaƙa: Gwamnan Kano ya bayar da umarnin farautar wanda ya kashe uwa da ’ya’yanta 6

Rundunar ƴan sandan ta bayyana sunayen mutanen da aka cafke da suka haɗa da Umar Auwalu mai shekaru 23 daga unguwar Sabuwar Gandu, Isyaku Yakubu wanda aka fi sani da Chebe mai shekaru 40 daga unguwar Sagagi, da Yakubu Abdulaziz wanda aka fi sani da Wawo mai shekaru 21 daga unguwar Sabon Gida Sharada, dukkansu a Kano.

Umar Auwalu, wanda ɗan’uwan matar da aka kashe ne, ya kasance jagoran ƙungiyar masu aikata laifin, inda bincike ya nuna shi ne ya tsara kisan, tare da danganta ƙungiyar da wasu hare-haren tashin hankali a Kano, ciki har da kisan wasu mata biyu da kona su a unguwar Tudun Yola.

Kayayyakin da aka kwato daga hannun mutanen sun haɗa da tufafi huɗu masu jini, wayoyin hannu biyu na mamatan, adda, gora, kuɗaɗen da ake zargin an sace daga wurin, da wasu makamai masu haɗari, yayin da bincike ke ci gaba domin gano cikakken girman ayyukan ƙungiyar.

Rundunar ƴan sandan Jihar Kano ta tabbatar wa al’ummar jihar kudirinta na ganin an gurfanar da duk masu hannu a aikata laifuka gaban shari’a domin tabbatar da adalci da tsaron rayuka da dukiyoyi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here