Da Dumi-Dumi: Hukumar Kwastam ta kama kayan laifuka daga Turkiyya zuwa Legas

Hukumar, Kwastam, kama, kayan, laifuka, Turkiyya, Legas
Hukumar Kwastam ta Najeriya ta kama makamai daban-daban da jirage masu saukar ungulu, da kayayyakin soji da kudinsu ya kai naira biliyan 1.5 da aka fitar...

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta kama makamai daban-daban da jirage masu saukar ungulu, da kayayyakin soji da kudinsu ya kai naira biliyan 1.5 da aka fitar daga Turkiyya zuwa Legas

Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam, Adewale Adeniyi ne ya bayyana hakan a Legas ranar Laraba a ofishin hukumar na Murtala Muhammed.

Ya ce rundunar tayi aiki bisa bayanan sirri na gida da waje masu hadin gwiwa a ranar 19 ga watan Yuni, 2024, ta tura jami’anta domin gano duk wuraren fita da ke kusa da filin jirgin.

Karin labari: ‘Yan ta’adda sun kashe babban dan wata alkalin kotu a Kaduna

Shugaban Kwastam din ya kuma bayyana darajar kayayyakin sojoji da na jami’an tsaro da aka shigo da su ba bisa ka’ida ba kan naira biliyan 1.29 wanda jimillar kayan ya kai biliyan 1.5.

Ya ce binciken da aka yi a baya-bayan nan ya nuna cewa wasu marasa kishin Najeriya da ke zaune a Turkiyya na saye da tattarawa da fitar da wadannan haramtattun makamai zuwa Najeriya.

Karin labari: Wani dalibin jami’ar tarayya dake Gombe ya rasa rayuwar sa, sakamakon musun ball

Adeniyi ya ce, an kama wanda ake zargi da laifin shigo da makamai ba bisa ka’ida ba, kuma za a mika shi ga Cibiyar Kula da Kananan Makamai ta Kasa, da ke karkashin ofishin mai ba Shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, domin gudanar da bincike da kuma gurfanar da shi gaban kotu.

Idan dai ba a manta ba a kwanakin baya ne hukumar kwastam ta sanar da cewa jami’anta a garin Fatakwal sun kama bindigu 844 da alburusai 112,500.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here