Kano: Gwamna Yususf Ya Soke Siyar da Asibitin Yara na Hasiya Bayero Da Gidan Gwamna.

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya soke sayar da asibitin kananan yara na Hasiya Bayero da kuma masaukin gwamna dake birnin Kwankwasiyya.

Yusuf ya ce ana ci gaba da kwato kadarorin al’umma da gwamnatin da ta shude ta sayar ba bisa ka’ida ba.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Gwamnan ya bayar da umarnin a gaggauta gyara ma’aikatar lafiya tare da mayar da aikinta a matsayin asibitin kwararru da ke kula da lafiyar dubban daruruwan yara daga jihar da sauran su.

Wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ta ce Abba Yusuf wanda ya jagoranci tawagar manyan jami’an gwamnati da suka kai ziyarar gani da ido a wuraren biyu da aka soke, ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda gwamnatin da ta shude ta sayar da wuraren ga ‘yan gidan su.

“Kamar yadda muka yi alkawari a lokacin zaben, ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen kwato kadarorin gwamnati ko dai an karkatar da su ko kuma a sayar da su ta hanyar bogi, abin da aka kwato za a yi amfani da shi cikin adalci don amfanin jama’ar jihar.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here