Gwamnatin Najeriya ta shiga wata ganawa da ƙungiyar ƙwadago ta TUC a Fadar gwamnati domin tattauna batun cire tallafin man fetur.
Wannan ɗorawa ne kan ganawar da suka yi da ƙungiyar NLC wadda aka tashi ba tare da cimma wata matsaya ba.
A taron, NLC ta nemi gwamnati ta koma sayar da man fetur kan farashin da aka saba kafin ta koma tattaunawa da kungiyar.
A taron na yau, tawagar gwamnatin tarayya ta samu jagorancin Sakataren gwamnati, Sanata Goerge Akume. Sauran sun haɗa da Gwamnan Babban banki, Godwin Emefiele da tsohon gwamnan jihar Edo, Kwamared Adams Oshiomhole da shugaban Kamfanin mai na Najeriya, Mele Kyari.
Akwai kuma mambobin ƙungiyar TUC guda bakwai ƙarƙashin jagorancin Mista Festus Osifo.












































