Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar kano ya jagirancin rushe shagunan da tsohon gwamnan kano Ganduje yayi a cikin filin idi na kano.
Rahotanni sun ce a Daren ranar lahadi gwamnan da ‘yan tawagar sa suka isa filin inda aka ragargaje dukkan shagunan da tsohuwar gwamnati ta gudanar a filin.
Gwamna Yusuf ya sha alwashin ruguje dukkan guraren da aka Gina ba bisa kaida ba.
Yusuf yace ” Ba daidai bane haka kawai wasu mutane marasa kishi su rika wawaso kan hakkin guraren jamaa ana kallon su sakaka suna abinda suke so”
Inda ya bukaci alumma dasu taimaka musu fallasa duk wasu bayanan sirri kan aikata ba daidai ba da tsohuwar gwamnatin Ganduje ta assasa.












































