Shugaban jam’iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano, Dakta Hashimu Dungurawa ya zargi shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu da hannu a hana ruwa gudu a rikicin masarautar Kano da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa tsakanin Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero.
Dakta Hashimu ya shaidawa manema labarai cewa yana da hujjojin da ke gasgata zarge-zargen da ya yi, inda ya ce “a bayyane take dangane da al’amarin da ke faruwa wanda kuma ke nuna sa hannun shugaban.
Karin labari: “Kamfanonin man fetur za su bada mai na wasu lokuta ga al’umma” – NNPC
“Tinubu saboda alakarsa da mahaifiyar tsohon sarkin, Aminu Ado Bayero, ya ce ba zai yarda ba dole sai an naɗa shi sarki. An kawo mana ƴan sanda da sojoji a birnin Kano a daidai lokacin da sauran sassan ƙasar suke fama da matsalar tsaro” in ji Dungurawa.
BBC ta tambayi shugaban jam’iyyar na NNPP na Kano dangane da hujjar da yake da ita kan zarge-zargen nasa sai ya ce “wane ne shugaban ƙasar Najeriya a yanzu? Ba Tinubu ba ne? Yaya za a yi a jibge ƴan sanda da sojoji na tsawon watanni ba tare da sanin shugaban ƙasa ba? Idan kuwa bai sani ba to akwai matsala.”
Karin labari: “Kamfanonin man fetur za su bada mai na wasu lokuta ga al’umma” – NNPC
Saidai jaridar ta tuntubi ɗaya daga cikin masu taimakawa shugaba Tinubu kan yaɗa labarai, Malam Abdu’aziz Abdul’aziz kan zarge-zargen, to amma har lokacin fitar da rahoton bai ce komai ba.