Rundunar Ƴan Sanda Sun Kama Ɓarayin Allunan Makabarta.

Rahotanni daga Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta tabbatar da kama wasu da ake zargi da satar allunan makabarta 28 da ake yi wa kabari shaidar mamata.

Cikin wata sanarwar da ta fitar da ke kunshe da irin nasarorin da ta cimma cikin kwanaki 12 da suka wuce, rundunar tace ta kama matasan dumu dumu suna karye allunan

A tattaunawar su da ɗaya daga cikin ɓarayin yace “Ina shiga Maƙabarta nayi satar Allunan Kabari da ƙarfe 03:00 na dare”- inji wannan matashin.

Bayan matsa masa da tambayoyi, matashin yace idan ya sayar yana amfani da kuɗin ne wajen sayen abincin da zaici da kuma taba Sigari

I zuwa yanzu rundunar tayi holin matasan dan cigba da bincike mai zurfi domin girbar abinda suka shuka.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here