SERAP ta buƙaci Tinubu ya hana Wike kulle ofisoshin Jakadanci 34 a Abuja

created by photogrid
created by photogrid

Ƙungiyar SERAP mai rajin tabbatar da adalci da daidaito a ayyukan gwamnati da ƴan majalisu, ta buƙaci Shugaban ƙasa  Bola Tinubu da ya shiga tsakani tare da dakatar da abin da ta bayyana a matsayin barazanar da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike ke yi na rufe ofisoshin jakadancin kasashen waje guda 34 da ke Abuja saboda rashin biyan kudin haraji filaye ga gwamnati.

A wani sako da ta wallafa a shafin X  a yau Litinin, SERAP ta yi gargadin cewa irin wannan matakin zai saba dokokin kasa da kasa da yarjejeniyoyin diflomasiyya.

SERAP ta ankarar da cewa, sashe na 22 na yarjejeniyar Vienna kan huldar diflomasiyya, wanda ke ba da tabbacin rashin cin zarafin ofisoshin diflomasiyya da kuma hana wuraren su zama batun bincike ko buƙatun da haɗawa ko kuma kisa.

Takaddamar dai ta samo asali ne daga wata fallasa da hukumar babban birnin tarayya ta yi na cewa akalla ofisoshin jakadanci 34 a Abuja ake bi bashin kuɗaɗen tun daga shekarar 2014.

Daga cikin ofisoshin jakadanci da aka jera a matsayin wadanda suka yi taurin bashin ki sun hada da Ghana da Thailand da Cote d’Ivoire sai Rasha da Philippines da Netherlands da Turkey da Guinea da kuma Ireland.

Sauran sun haɗa da: Uganda da Iraq da Zambia da Tanzania da Jamus da DR Congo, sai Venezuela da Korea da Trinidad da Tobago Sai Egypt da Chad da India da Sudan da Kenya da Zimbabwe da Ethiopia kuma Indonesia.

Haka kuma akwai: Tarayyar Turai da Switzerland da Saudi Arabia da China da Afirka ta Kudu, da Equatorial Guinea.

Ministan babban birnin tarayya, Wike, a cikin umarnin da ya bayar a ranar 26 ga watan Mayu, ya ba da umarnin daukar matakin kulle wurare da kaddarori guda 4,794 da ba a biya kudin harajin Kasar ba tsakanin shekaru 10 zuwa 43.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here