Gwamna Abba ya gargadi kungiyoyi masu yunkurin auren jinsi a Kano

Abba, Kabir, Yusuf, gargadi, kungiyoyi, yunkurin, auren, jinsi, Kano
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya umarci hukumar Hisbah ta jihar da ta murkushe kungiyoyin da ake zargi da tallatawa da ykare hakkin LGBTQ a Kano...

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya umarci hukumar Hisbah ta jihar da ta murkushe kungiyoyin da ake zargi da tallatawa da ykare hakkin LGBTQ a Kano.

Umarnin dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta samun tashe-tashen hankula game da ayyukan kungiyoyin da ake zargin suna inganta auren jinsi a jihar.

Kwamishinan yada labarai, Baba Halilu Dantiye ne ya bayyana hakan a ranar Litinin da ta gabata yayin da yake magana kan damuwar da ‘yan kasar suka nuna.

Karin labari: Shugaban NNPP na Kano ya zargi Tinubu da goyon bayan Aminu Ado Bayero

A cewar kwamishinan, ayyukan kungiyar mai suna “WISE” ko “Women Initiative for Sustainable Empowerment and Equality” ya sabawa ka’idojin jihar da kuma sabawa shari’a.

Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ba za ta amince da duk wata yarjejeniya da za ta inganta ayyukan ‘yan luwadi da madigo ba, saboda ya sabawa ka’ida da dabi’un mutanen Kano.

“Na yi magana da gwamna, kuma ya nuna rashin amincewarsa da yarjejeniyar da aka ce, ko da yake ba a tabbatar da hakan ba. Ya kuma tabbatar min da cewa babu inda ake gudanar da ayyukan LGBT a Kano,” in ji Dantiye.

Karin labari: Shugaban NNPP na Kano ya zargi Tinubu da goyon bayan Aminu Ado Bayero

“Kamar yadda kuka sani, kashi 98 na mutanen Kano Musulmi ne bisa imani, kuma addininmu ya sabawa wannan fasikanci, don haka ba za mu yarda da shi ba,” in ji shi.

Kwamishinan ya ce gwamnati ta samu damuwar ‘yan kasar kan kungiyoyin da ke yada ayyukan LGBT a jihar kuma gwamnan ya umarci hukumar Hisbah ta gudanar da bincike tare da daukar mataki kan wadannan kungiyoyin.

“Mun kuma tattauna da gwamnan kan hakan, kuma ya umurci Hisbah ta yi bincike tare da murkushe su. Za mu dauki matakin shari’a yadda ya dace,” inji shi.

Dantiye ya kuma bayyana cewa ana ci gaba da tuntubar malaman addini kan yadda za a dakile irin wadannan ayyuka a jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here