Majalisar wakilai ta bukaci gwamnatin tarayya da ta dakatar da aiwatar da yarjejeniyar auren jinsi har sai an magance duk wasu batutuwan da ke janyo cece-kuce.
Hakan ya biyo bayan kudirin gaggawa na muhimmancin kasa da ‘yan majalisar 88 suka dauki nauyi.
Da yake gabatar da kudirin a ranar Talata, dan majalisar, Aliyu Madaki, ya ja hankali kan maganar da ke nuna “daidaitan jinsi” tare da bayyana shi a matsayin dokin Trojan da ka iya cin zarafin al’ummar kasar nan.
Majalisar ta kuma umarci kwamitocin ta da su binciki kudurorin yarjejeniyar da ke cike da cece-kuce.
Karin labari: “Ba za mu tafi yajin aiki ba idan muka cimma matsaya da gwamnatin Tarayya” – ASUU
Takaddama dai ta kunno kai kan yarjejeniyar Samoa da gwamnatin tarayya ta rattaba hannu da kungiyar Tarayyar Turai, inda da dama suka nuna rashin jin dadinsu kan yadda gwamnatin Najeriya ta amince da ‘yancin masu fasukanci
Yarjejeniyar Samoa ta haifar da cece-kuce a yanar gizo tare da wasu da dama da ke adawa da yancin LGBT, wanda ya sabawa dokar hana auren jinsi da ma’auratan da aka kafa a shekarar 2014 da shugaba Goodluck Jonathan ya yi a lokacin.
Karin labari: Gwamna Abba ya gargadi kungiyoyi masu yunkurin auren jinsi a Kano
A taron manema labarai a ranar Asabar, ministan kasafi da tsare-tsare na tattalin arziki, Atiku Bagudu, tare da takwaransa na ma’aikatar yada labarai, Mohammed Idris, ya ce Najeriya ba za ta kulla wata yarjejeniya da ta sabawa kundin tsarin mulki ba da kuma fahimtar addini da al’adu na al’ummar Najeriya daban-daban.
Bagudu ya ce Najeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar ne domin bunkasa samar da abinci, da habaka tattalin arzikin da ya hada da sauran muhimman fannoni.
Najeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a ranar 28 ga watan Yunin 2024, amma ya zama abin sani ga jama’a a wannan makon bayan da Bagudu ya bayyana hakan.