Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta ce yajin aikin da suke shirin yi ba lallai ya tabbata ba, idan Gwamnatin Tarayya ta aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma, nan da makonni biyu masu zuwa.
Farfesa Emmanuel Osodeke, shugaban kungiyar ASUU ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a ranar Litinin.
Idan dai za a iya tunawa, ASUU ta yi barazanar shiga yajin aikin saboda rashin aiwatar da yarjejeniyoyin da suka cimma da gwamnatin tarayya.
Ministan Ilimi Farfesa Tahir Mamman ya gayyaci kungiyar a ranar 26 ga watan Yuni domin tattaunawa kan matsalolin da suka dabaibaye jami’o’i da kuma dakile yajin aikin da suke shirin yi.
Karin labari: Sojoji da mafarauta sun dakile yunkurin ‘yan tada kayar baya a Yobe
Osodeke ya ce babu daya daga cikin yarjejeniyoyin da aka cimma da gwamnatin tarayya da aka aiwatar.
“A taron da Ministan Ilimi ya kira mun amince cewa bayan mako biyu za mu hadu domin ganin ci gaban da gwamnati ta samu.
“Za kuma mu ga abin da za mu yi na gaba idan gwamnati ta gaza aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma.
“Taron a cikin makonni biyu masu zuwa shi ne don ganin abin da suka yi wanda zai sanar da shawararmu,” in ji shi.
Shugaban ASUU ya ce wasu daga cikin bukatun sun hada da rashin aiwatar da yarjejeniyoyin da aka sake tattaunawa a shekarar 2009.
Karin labari: Gwamnatin tarayya ta ware naira biliyan 732 cikin kasafin kudin 2024 na karfafa wasu ayyuka
Ya ce an shafe sama da shekaru shida ana kulla yarjejeniyar, kuma har yanzu gwamnati ba ta aiwatar da su ba.
Osodeke ya ce alawus-alawus din karatun da ‘ya’yan su ke biya su ma sun taru sama da shekaru shida kuma ba a yi komai a kai ba.
Dangane da batun asusun farfado da tattalin arzikin, ya ce sun amince da rahoton tantance bukatu na tara Naira biliyan 200 a duk shekara, har tsawon shekaru biyar.
Oshodeke ya kara da cewa har yanzu gwamnati ba ta hana yaduwar jami’o’i ba, ya kara da cewa ana amincewa da sabbin jami’o’i da dama ba tare da kudaden gudanar da su ba.
Ya ce har yanzu gwamnati ba ta daina biyan albashin jami’o’i daga tsarin hada-hadar ma’aikata da tsarin biyan albashi na (IPPIS) kamar yadda majalisar zartarwa ta tarayya ta amince a watan Janairu.
Ya ce har yanzu IPPIS na biyan mambobinsu albashi sabanin umarnin da hukumar ta FEC ta bayar kamar yadda NAN ta bayyana.