Gwamnatin tarayya ta ware naira biliyan 732 cikin kasafin kudin 2024 na karfafa wasu ayyuka

Tinibu, gwamnatin, Najeriya, tarayya, ware, naira, biliyan, kasafin, kudin, karfafa, ayyuka, kiwon, lafiya
Ana zargin gwamnatin Tarayyar Najeriya da ware Naira biliyan 732 kan ayyukan karfafa gwiwa fiye da Naira biliyan 646.5 da aka ware wa ayyukan kiwon lafiya...

Ana zargin gwamnatin Tarayyar Najeriya da ware Naira biliyan 732 kan ayyukan karfafa gwiwa fiye da Naira biliyan 646.5 da aka ware wa ayyukan kiwon lafiya a cikin kasafin kudin kasar na 2024.

A cewar wata sanarwa daga Ayomide Ladipo, shugaban Tracka, wani reshen BudgIT, hukumar ta ce ayyukan karfafawa Najeriya ba su da tabbas kuma suna da kalubalen ganowa saboda yanayin su.

Ya yi nuni da cewa, za a yi amfani da dimbin kason na ayyukan karfafawa ne domin dakile gibin da ake samu a fannin kiwon lafiyar Najeriya da ke da matsayi na biyu a yawan mace-macen yara a duniya.

Karin labari: Yadda jihohin Arewacin Najeriya ke fuskantar barazarar ambaliyar ruwa

Traka ya kuma bukaci hukumomin yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya da su binciki wadannan matsalolin da ke cikin kasafin kudin 2024 don dakile karkatar da almubazzaranci.

Idan ba’a manta ba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kudin shekarar 2024 na Naira tiriliyan 28.7 ya zama doka a watan Janairun wannan shekara.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here