Dakarun Operation Fasan Yamma na rundunar sojin saman Najeriya, sojojinta tare da haɗin gwiwar ƴan sa-kai sun samu nasara a wata fafatawa da suka yi da ƴan bindiga a ƙayukan Ragada da Warari da ke Jihar Neja.
Rundunar ta ce a lokacin artabun, wadda ta faru a jiya Talata ta kashe fiye da ‘yan bindiga 95 waɗanda ke yawo akan babura, da lamarin ya biyo bayan da sojojin suka samu sahihan bayanai daga mazauna yankin game da hanyoyin da ‘yan bindiga ke bi don satar shanu.
Haka kuma runduna ta ce, bata garin na tare da a kan babura guda 108 dauke da muggan makamai inda suka nufi Warari da kuma karamar hukumar Rijau.
Rahotonni sun bayyana cewa, cikin yan bindigar su 108 guda 13 kadai suka iya tserewa inda dakarun suka samu nasarar hallaka masu yawan daga cikinsu.













































