Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda, ta amince da karin girma ga Sufetocin rundunar akalla su 4,741 bayan ganawar da ta yi da su a baya-bayan nan a fadin kasar nan.
Akalla jami’ai 4,708 ne aka kara wa girma zuwa mataimakan Sufurtandan ‘yan sanda wadanda ba a tabbatar da su ba a baya, yayin da 33 suka samu karin girma zuwa manyan sufeto.
A cewar mai magana da yawun hukumar, Ikechukwu Ani, a yau Laraba, hukumar ta kuma amince da karin girma ga mataimakan sufiritandan ‘yan sanda 38 zuwa Sufurtanda sai kuma wasu masu mukamin Sifurtanda guda 29 zuwa manyan Sufurtanda.
Tun da farko dai hukumar ta yi nazari tare da amincewa da karin girma ga kwamishinonin ‘yan sanda 12 zuwa matsayi na gaba na mataimakan sufeto janar, sai mataimakan kwamishinoni 16 zuwa kwamishinoni, da mataimakan kwamishinoni 28 zuwa manyanm mataimakan kwamishinoni.
“Shugaban hukumar DIG Hashimu Argungu, ne ya jagoranci taron, wanda ya samu halartar mai shari’a Paul Adamu Galumje, mai ritaya wanda a baya ya yi aiki a kotun koli, wanda ke wakiltar bangaren shari’a a hukumar sai DIG Taiwo Lakanu mai ritaya wanda ke wakiltar ‘yan sanda a hukumar, sai kuma mai shari’a Christine Ladi Dabup mai ritaya daga babbar kotun jiha.
“Sauran mambobin su ne Abdulfatah Mohammed da Cif Onyemuche Nnamani da Sakataren Hukumar.
Sabbin Sufetocin da aka kara wa girma sun hada da Rabiu Ibrahim da Izang Nyam sai Nannim James da Chinelo Obinuku da Bariminas Auyatiya da Sabi’u Umar.
“Sauran su ne Lawan Haruna da Opurum Patrick da Agbo James da kuma Georgewill Onwubiko da sauransu.
Shugaban Hukumar, DIG Argungu, ya nanata kudurinsa na nuna kishin kasa da kishin aiki tare da sadaukar da kai ga jama’a musamman wajen mu’amalarsu ta yau da kullum ga jama’a.












































