Neja: Cutar Kwalara ta kashe mutane 12 tare da jikkata wasu fiye da 230

Cholera Adamawa

Ɓarkewar cutar Amai da Gudawa watau kwalara a jihar Neja ta yi sanadin mutuwar mutane akalla 12 tare da jikkata wasu fiye da 230 a wasu ƙananan hukumomin jihar.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN, ya ruwaito cewa an fara gano bullar cutar ne a ranar Lahadi a karamar hukumar Shiroro.

Ya zuwa yau Laraba, Rahotonni sun ce an samu bazuwar annobar zuwa aƙalla ƙananan hukumomi shida, da suka hada da Minna da Bosso da Shiroro da Magama Sai Bisa da kuma Munya.

Jami’an kiwon lafiya sun ce mutane 239 lamarin ya shafa kuma a halin yanzu suna karɓar magani a cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko a yankunan da abin ya shafa.

A martanin da gwamnatin jihar ta mayar, ta ce, ta bude cibiyar killace mutanen da suka kamu da cutar a tsohon reshen cibiyar kula da lafiya matakin farko na marigayi Sanata Idris Kuta da ke Minna.

Kwamishinan lafiya a matakin farko, Dakta Ibrahim Dangana, ya tabbatar da cewa an tura tawagar da ta ƙunshi ɓangarori da dama domin daƙile yaɗuwar cutar.

Ya yaba wa Gwamna Mohammed Bago, bisa gaggauta ɗaukar mataki kan lamarin tare da yaba wa da tallafin da hukumomin bayar da agaji ke ba su.

Shi ma da ya ke jawabi, Daraktan kiwon lafiyar Jama’a a ma’aikatar lafiya ta jihar Dakta Ibrahim Idris, ya bayyana yankunan Chanchaga da Minna da Bosso da Shiroro a matsayin wuraren da cutar ta fi yin ƙamari.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here